Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
MDD da AU sun yi Allah wadai da harin kunar bakin wake a Mogadishu
2019-07-25 10:29:54        cri

Manyan jakadun MDD da kungiyar tarayyar Afrika AU dake kasar Somalia, sun yi Allah wadai da harin kunar bakin wake wanda aka kaddamar a ofishin magajin garin birnin Mogadishu a ranar Laraba.

A cikin sanarwar da suka fitar, James Swan, wakilin musamman na babban sakataren MDD dake Somalia, da Francisco Madeira, wakilin musamman na shugaban gudanarwar kungiyar tarayyar Afrka dake Somalia, sun bayyana cewa, harin ya nuna rashin imani da rashin tausayi ga rayuwar bil Adama.

An shirya kaddamar da harin kunar bakin waken ne a daidai lokacin da ake wani taro a harabar ofishin magajin garin, mutane 6 sun mutu kana ba'a bayyana adadin mutanen da suka jikkata a sanadiyyar harin ba.

Magajin garin birnin Abdirahman Omar Osman, yana daga cikin mutanen da suka samu raunuka bayan da abubuwan fashewar suka tarwatse inda suka buge shi a daidai cikinsa.

Mayakan kungiyar al-Shabab, sun dauki alhakin kaddamar da harin, inda suka bayyana cewa, sun kaddamar da harin ne da nufin hallaka wakilin MDD wanda suka ce sun yi amanna yana cikin harabar ofishin magajin garin.(Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China