![]() |
|
2020-03-28 16:00:13 cri |
Jakadan kasar Sin dake Najeriya, Zhou Pingjian, da wasu jami'an ma'aikatar harkokin wajen kasar ne suka halarci bikin bada kayayyakin.
Jakada Zhou Pingjian, ya bayyana cewa, gwamnati da jama'ar Najeriya sun nuna goyon baya tare da tallafawa kasar Sin ta hanyoyi daban daban a yayin da take cikin mawuyacin hali na yakar cutar COVID-19, kuma kasar Sin ba za ta manta ba. Ya ce Sin na cike da imanin cewa, Najeriya za ta cimma nasarar yakar cutar, kuma tana son karfafa hadin kai da kasar a fannonin da suka shafi kandagarki da shawo kan cutar da dai sauransu.
A nasu bangaren, jami'an Najeriya, sun yi godiya da tallafin da Sin ke samarwa a wannan muhimmin lokaci. A cewarsu, wannan ya nuna cewa, dangantakar dake tsakanin kasashen biyu tana da kyau kwarai. Baya ga haka, sun bayyana cewa, matakan yakar annobar na kasar Sin, sun zama abun misali ga kasashe daban daban, kuma amincewa da goyon bayan da Sin ta ba Najeriya, sun karfafa imanin kasar na tinkarar annobar. (Bilkisu)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China