2020-03-24 10:43:05 cri |
Hukumar MDD mai kula da tattalin arzikin Afirka(UNECA) ce ta bayyana haka cikin wata sanarwa, tana mai cewa, ministocin kudin kasashen na Afirka da suka gana da kafar bidiyo, saboda fargabar COVID-19, sun kuma yi musayar ra'ayoyi kan matakan da gwamnatocinsu ke dauka, don magance tasirin cutar kan zamantakewa da tattalin arziki.
Sanarwar bayan taron da hukumar ECA ta fitar na cewa, ministocin sun kuma lura da cewa, kafin barkewar cutar, nahiyar tana fuskantar gibin kudaden da za a yi amfani da su wajen daukar matakai da shirye-shiryen cimma nasarar muradun karni da ajandar raya nahiyar nan da shekarar 2063.
Bugu da kari, ministocin sun jaddada cewa, muddin ba a hada kai ba, hakika cutar COVID-19 za ta yi mummunar tasiri kan tattalin arziki da zamantakewar al'ummomin nahiyar baki daya.
Don haka, sun jaddada bukatar yin aiki da WHO da hukumomin nahiyar, musammam kungiyar tarayyar Afirka(AU) da cibiyar kandagarki da hana yaduwar cututtuka ta Afirka(Africa CDC), a hannu guda kuma a yi kyakkyawan amfani da tsare-tsare da abokan hulda dake ba da tallafi, kamar asusun kasa da kasa.(Ibrahim)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China