2020-03-23 19:09:16 cri |
Mr. Bill de Blasio, ya soki shugaba Trump da cewa, "miliyoyin Amurkawa ba su gane me kake yi ba. A lokacin da kasarmu ta tsunduma cikin mawuyacin hali, ba ka gudanar da aikinka yadda ya kamata". Ya ce "A yayin da ake fuskantar barkewar annoba, kamata ya yi a hada karfin kowa da kowa, amma ba mu san dalilin da ya sa ka yi ta tsayawa kana kallo ba. Ga shi ka rasa damar ceton kasar Amurka."
Mr. Bill de Blasio ya kara da cewa, nan da sati biyu zuwa uku, kayayyakin jinya da ake bukata wajen shawo kan cutar za su kare, don haka ba yadda za a yi illa a hada karfi da bangaren sojojin kasar don biyan bukatun da ake da su. Sai dai har yanzu, rundunar sojan da ta fi karfi a duniya ba ta fara aiki ba.(Lubabatu)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China