Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin za ta baiwa WHO tallafin dala dubu 100 don samarwa Sudan ta kudu kayayyakin kariyar COVID-19
2020-03-23 09:25:46        cri

Ofishin jakadancin kasar Sin dake kasar Sudan ta kudu, ya sanar da anniyarsa ta baiwa hukumar lafiya ta duniya WHO a takaice gudummawar dala dubu 100, don samar da kayayyakin kariya da na kiwon lafiya, a wani mataki da yaki da cutar Cutar COVID -19 a kasar Sudan ta kudu.

Jakadan kasar Sin dake Sudan ta kudu Hua Ning ne, ya bayyana haka cikin wata sanarwa a birnin Juba, fadar mulkin kasar. Yana mai cewa, babban kalubalen da kasar ke fuskanta, shi ne kandagarki da hana yaduwar cutar da ake shigo da ita daga ketare.

Hua ya ce, za a yi amfani da gudummawar wajen sayen kayayyaki, ciki har da na kiwon lafiya da kasar take matukar bukata cikin gaggawa.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China