2020-03-11 11:08:32 cri |
Modou Njie, daraktan sashen bunkasa kiwon lafiya da ilmantar da alluma na ma'aikatar lafiyar kasar, ya ce gudunmawar za ta taimakawa kasar wajen cike gibin da ake da shi wajen isar da muhimman kayayyakin kiwon lafiya zuwa yankunan karkara.
Modou ya ce suna da likitoci, da nas-nas, kuma suna da kwararrun masana kiwon lafiya a asibitoci, a dukkan bangarorin asibitin koyarwa na Edward Francis (EFSTH) dake Banjul da babban asibitin Serekunda dake Kanifing. Amma hanyoyin da za'a isa zuwa asibitocin shi ne babban kalubale, don haka wadannan motoci za su taimaka wajen magance matsalolin. (Ahmad Fagam)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China