Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
MDD: Farin dango sun shiga kasashe 9 a nahiyar Afirka
2020-02-28 11:20:28        cri
Mai Magana da yawun MDD Stephane Dujarric, ya bayyana cewa, farin dango masu lalata amfanin gona suna ci gaba da shiga Jamhuriyar demokiradiyar Congo (DRC) da yankin tekun fasha ta gabashin Afirka.

Kasashen da farin suka mamaye sun, sun hada da Djibouti, da Eritrea da Habasha, da Kenya da Somaliya da Sudan ta kudu, da Tanzaniya da Uganda, da yankin gulf, sai kuma 'yan kalilan da suka shiga DRC.

Dujarric ya ce, tuni farin suka lalata dubban daruruwan eka na gonaki, ciki har da filayen noma da na kiwo. A don haka, ofishin kula da harkokin jin kai na MDD (OCHA) ya yi gargadin cewa, kananan farin da ke kokarin girma, za su fara barna a farkon lokacin damina, lokaci mafi muhimmanci na shuka a wasu kasashen da matsalar ta shafa da wadanda ke fuskantar barazanar farin a gabashin Afirka.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China