Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An bukaci nahiyar Afrika ta yaki da cin hanci da rashawa domin cimma muradun ci gaba masu dorewa
2020-02-26 10:45:31        cri
An bukaci nahiyar Afrika ta yaki da cin hanci da rashawa da inganta tsaro da zaman lafiya, domin gaggauta cimma muradun ci gaba masu dorewa.

Shugaban Zimbabwe, Emmerson Mnangagwa ne ya yi kiran a jiya, yayin bude taron Afrika karo na 6 kan ci gaba mai dorewa, dake gudana a garin Victoria Falls.

Ana gudanar da taron wanda za a kammala a gobe, domin nazarin nasarorin da nahiyar ta samu wajen aiwatar da muradun.

Emmerson Mnangagwa ya ce, yadda ake fama da cin hanci na tarnaki tare da illata ci gaban nahiyar, da kuma ingantuwar zaman takewar al'umma.

Ya ce dole ne nahiyar ta ci gaba da kokarin wanzar da tsaro da zaman lafiya ta hanyar kawar da makamai da kawo karshen dukkan nau'ikan rikici.

Ya ce dole ne nahiyar ta lalubo damarmakin da take da su a bangarorin aikin gona da hakar ma'adinai da bangarori masu zaman kansu, da aiwatar da dabarun yaki da sauyin yanayi da zuba jari a fannonin fasaha da karfafa bangaren, domin gaggauta cimma muradun ci gaba masu dorewa. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China