Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ghana ta dakatar da jami'an gwamnati daga tafiya kasashen waje na wani lokaci
2020-03-11 10:07:30        cri
Shugaban kasar Ghana, Nana Akufo-Addo, ya bada umarnin dakatar da jami'an gwamnati daga tafiye-tafiye zuwa ketare na wucin gadi, a wani mataki na kandagarkin cutar COVID-19.

Wata sanarwa da shugaban ma'aikatansa, Akosua Frema Osei-Opare ya fitar, ta ce tafiye-tafiye masu tsananin muhimmanci ne kadai za iya la'akari da su.

A cewar sanarwar, umarnin da sauran matakan da gwamnati ta dauka, na da nufin kare al'umma daga kamuwa da kwayar cutar.

Umarnin na zuwa ne raneku bayan shugaban na Ghana, ya sanar da daukar wasu makatai na kare al'ummar kasar daga cutar COVID-19. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China