Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
2019: 'Yan Ghana 828 sun ci gajiyar tallafin horaswa na Sin
2019-12-26 09:31:02        cri
Ofishin jakadancin Sin dake kasar Ghana, ya ce 'yan kasar ta Ghana 828 ne suka ci gajiyar samun horo da sanin makamar aiki a sassa daban daban, karkashin tallafin da Sin ke daukar nauyi cikin shekarar nan ta 2019.

Wata sanarwar da ofishin ya fitar ta nuna cewa, sassan da mutanen suka ci gajiyar samar da horon na Sin, sun hada da na rage talauci, da kiwon lafiya, kuma hakan daya ne daga ginshikan raya hadin gwiwa tsakanin Sin da kasar Ghana.

Sanarwar ta kara da cewa, daga shekarar 2018 zuwa yanzu, sama da 'yan Ghana 7,100 ne aka gayyata kasar Sin, domin halartar horo, da tarukan karawa juna sani daban daban.

Da yake karin haske game da hakan, daya daga cikin wadanda suka ci gajiyar wannan manufa, kuma jami'in hulda da jama'a a ofishin hukumar wanzar da ci gaba ta Ghana George Kwabena, ya ce horaswar da Sin ke samarwa, na ba da damar koyi daga kwarewar samar da ci gaba ta Sin, wadda ita ma Ghana na iya amfani da ita wajen raya kanta.

Kwabena ya ce "Mun kara fahimtar al'adun kasar Sin, da akidun raya al'umma, matakan da suka kara bude mana idanu a fannin gudanar da harkokin jama'a yadda ya kamata". (Saminu Hassan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China