Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ghana tana samun nasarori a shirin kare gandun daji
2019-12-21 15:51:56        cri
Wani babban jami'in kula da gandun daji na kasar Ghana ya ce, kokarin da kasar ke yi wajen kiyaye nau'in dabbobin dajin kasar yana samun kyawawan sakamako.

Kwadwo Owusu-Afriyie, shugaban hukumar kula da gandun dajin kasar Ghana, ya ce a bisa alkaluman binciken da aka gudanar sun nuna cewa da yawa daga cikin nau'ikan dabbobin dajin kasar, kamar giwaye da dabbar buffalos, ana samun nasarar kiyaye su.

Domin tabbatar da kiyaye muhallin halittu don kare nau'ikan dabbobin daji dake barazanar bacewa daga kasar, ya ce, hukumar tana daukar kwararan matakai domin ceto gandun dajin kasar baki daya.

Ya ce hukumar ta bayar da aikin kwangilar shuka bishiyoyi kimanin miliyan 25 ga 'yan kwangila 654 a fadin kasar.

Owusu-Afriyie ya ce, irin ci gaban da ake samu wani muhimmin al'amari ne game da yunkurin kasar na riga kafin matsalolin sauyin yanayi. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China