Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Tedros Adhanom Ghebreyesus ya yi alhinin rasuwar likitan kasar Sin da ya taka rawar gani wajen yaki da cutar COVID-19
2020-02-19 13:23:34        cri
Babban daraktan hukumar lafiya ta duniya WHO, Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya bayyana matukar alhininsa ga rasuwar babban jami'in daya daga asibitocin dake yaki da cutar numfashi ta COVID-19 a birnin Wuhan inda cutar ta fi kamari.

A sakon sa na Tiwita, Mr Ghebreyesus ya mika sakon ta'aziyyar sa ga iyalai, da sauran abokai, da ma sauran marasa lafiya dake amfana da gudummawar Dr. Liu Zhiming.

Dr. Liu Zhiming ya rasu ne a jiya Talata, bayan fama da cutar numfashi da ya harbu da ita, yayin da yake tsaka da taimakawa yakin da ake yi da cutar. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China