Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin za ta dawo da harkokin sufuri a yankunan da babu barazanar annobar COVID-19
2020-02-21 20:30:23        cri
Jami'i a ma'aikatar harkokin sufuri ta kasar Sin Xu Chengguang, ya bayyana cewa, gwamnati za ta dawo da harkokin sufurin jama'a a larduna da birane da ba sa fuskantar barazanar annobar COVID-19, wadanda a baya aka dakatar.

Ya ce, duba da managartan matakan da aka dauka, da ma nasarorin da aka samu na dakile yaduwar cutar, za a dawo da hidimomi na sufurin jama'a, ciki har da motocin safa-safa, da jiragen kasa gadan-gadan a yankunan da ke da karancin hadarin wannan annoba.

Jami'in ya bayyana haka ne yayin taron manema labarai da aka gudanar a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin. Ya zuwa jiya Alhamis, yankuna 26 a matakan larduna sun dawo da sufurin motocin fasinja tsakanin larduna, gami da wasu yankuna 30 a matakan larduna da nan ma aka dawo da zirga-zirgar motocin fasinja.

Ko da yake ba a dakatar da hidimar sufuri a birane 40 ba, yayin da yankuna 78 a matakan birane suka dawo da harkokin sufuri yadda ya kamata.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China