Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ma'aikatan jinyar kasar Sin sun cancanci yabo
2020-02-21 11:53:18        cri
Zuwa karshen jiya Alhamis, gaba daya akwai mutum 18264, wadanda aka sallame su daga asibiti bayan da suka warke daga cutar numfashi ta COVID-19 a babban yankin kasar Sin, kana a cikin kwanaki 9 a jere adadin mutanen da suka warke daga cutar a kowace rana ya zarce dubu 1. An tura ma'aikatan jinya sama da dubu 30 daga sassa daban-daban na kasar zuwa lardin Hubei, domin tallafawa ayyukan dakile yaduwar cutar. Ya zuwa ranar 11 ga wata, akwai ma'aikatan jinya 3019 a duk fadin kasar, wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar, ciki har da mutum 5 da suka rasa rayukansu.

Akwai ma'aikatan jinya da dama a kasar Sin, wadanda suka bar iyalansu suka sadaukar da kai domin halartar ayyukan shawo kan cutar COVID-19. Irin jajircewa da gudummawar da ma'aikatan jinyar suka bayar ya burge al'ummar kasar kwarai da gaske, inda aka yi kira da a in iyakacin kokarin kare muradunsu.

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya kuma jaddada cewa, ya zama dole a maida hankali da cikakkiyar kulawa, da kariya ga ma'aikatan jinya, don tabbatar da ganin suna aiwatar da ayyukansu lami-lafiya. Ya zuwa ranar 13 ga wata, hukumomin kudin kasar sun ware zunzurutun kudade da yawansu ya kai Yuan biliyan 25.94, domin sayen kayan jinya, da na kariya iri daban-daban, da kyautata na'urorin aikin jinya a asibitoci daban-daban. (Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China