Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Masu zuba jari na ketare na kara sha'awar zuba jari a Sin duk da annobar COVID-19
2020-02-21 20:08:46        cri
Darekta a sashen harkokin zuba jari na ketara a ma'aikatar kasuwancin kasar Sin Zong Changqing, ya bayyana cewa, kasar Sin na ci gaba da janyo hankulan masu sha'awar zuba daga ketare, saboda tasirin annobar COVID-19 ba mai dorewa ba.

Zong wanda ya bayyana haka ga taron manema labarai ta kafar Intanet, ya ce barkewar annobar ba ta illata tabbacin galibin manyan kamfanoni na zuba jari a cikin kasar ko shafar dabarunsu na zuba jari ba.

Ya ce, gwamnati tana da tabbacin da ma imanin daidaita harkokin zuba jari na ketare a wannan shekara. Bayanai sun nuna cewa, a shekarar da ta gabata, jarin kai tsaye na ketare da aka zuba a cikin kasar ya karu da kaso 4 cikin 100 kan makamancin lokaci na bara, idan aka kwatanta da kaso 4.8 cikin 100 da aka samu a watan Janairun shekarar 2019. Tasirin bullar annobar kan jarin waje ya fara fitowa, an yi hasashe cewa, zai karu a watannin Fabrairu da Maris.

Yayin da kasar Sin ta himmatu wajen ganin bayan wannan cuta, hukumomi sun kara karfafa matakai na taimakawa kamfanoni na ketare wajen ganin sun dawo bakin aiki da ma gudanar da ayyukansu ba tare da wata matsala ba.

Wata sanarwa da ma'aikatar kasuwancin kasar ta fitar a makon da ya gabata, ta jaddada goyon bayan ayyuka masu jarin waje, tana mai kira da a bullo da managartan matakai na magance bambance-bambancen dake tsakaninsu da rage tasirin wannan annoba.

Ya kara da cewa, ma'aikatar za ta tsarawa kananan hukumomin matakan taimakawa kamfanoni masu jarin waje, ta yadda za su ci gajiyar manufofin da aka tsara, da kare 'yanci da muradunsu, da kara ba su damar shiga kasuwannin hannayen jari da inganta yanayi na kasuwanci. (Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China