Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
AU ta jaddada aniyarta na tallafawa Sudan ta kudu wajen aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiya
2020-02-21 11:25:13        cri
Tawagar wakilan kungiyar tarayya Afrika (AU) sun bayyana cikakken goyon bayan kungiyar ga Sudan ta kudu a matsayinta na kasa mafi yarinta a duniya wajen aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiyar kasar da kafa gwamnatin rikon kwaryar kasar.

Tawagar majalisar zaman lafiya da wanzar da tsaro ta AU wato (PSC), a ranar Alhamis ta kammala wata ziyarar rangadi ta kwanaki uku a Sudan ta kudu, wanda aka shirya karkashin manufar majalisar na tabbatar da tsaro da zaman lafiyar nahiyar Afrika.

An rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiyar ta Sudan ta kudu (R-ARCSS) a ranar 12 ga watan Satumbar 2018, kuma ake da niyyar kafa gwamnatin hadin kan kasa wato (R-TGONU) a ranar 22 ga watan Fabrairun shekarar 2020.

Babbar manufar tawagar ta AU ita ce gudanar da bincike da kuma bibiyar matsayin aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiyar da kafa gwamnatin hadin kan kasa, wato R-TGONU da nufin samar da dawwamamman zaman lafiya, da kwanciyar hankali, da hadin kan al'umma, da kuma cigaba a Sudan ta kudu.

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China