2020-02-10 09:17:47 cri |
Shugaban Afrika ta kudu Cyril Ramaphosa, ya karbi ragamar shugabancin karba-karba na Tarayyar Afrika (AU), yayin bude taron shugabannin kasashe da gwamnatoci na tarayyar da ya gudana jiya a hedkwatarta dake birnin Addis Ababa na Habasha.
Taken taron karo na 33 dake gudana a kasar dake gabashin Afrika shi ne "Kawar da makamai: samar da kyakkyawan yanayi ga ci gaban Afrika."
Cyril Ramaphosa ya karbi ragamar shugabancin ne daga hannun shugaban Masar, Abdel Fattah al-Sisi.
Da yake jawabin karbar ragamar, shugaba Ramaphosa ya ce zai yi kokarin inganta batutuwan da Afrika ta sa a gaba na samun ci gaba da zaman lafiya, ta hanyar kara zurfafa dangantaka tsakanin kasashe mambobin tarayyar. (Fa'iza Mustapha)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China