Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
AU ta damu da yadda kungiyoyin 'yan ta'adda ke karuwa a yankin Sahel
2020-02-11 10:04:30        cri
Kwamishinan kungiyar tarayyar Afirka mai kula da harkokin zaman lafiya da tsaro Smail Chergui, ya bayyana cewa, kungiyar ta damu matuka da yadda kungiyoyin 'yan ta'adda ke karuwa a yankin Sahel.

Da yake karin haske kan haka a gefen taron kolin kungiyar karo na 33 da ya hallara shugabannin kasashe da gwamnatoci a birnin Addis Ababa na kasar Habasha, Chergui, ya ce, kungiyar ta lura da abubuwan dake faruwa da ma barazanar dake karuwa a yankin. Yana mai cewa, ba ma kawai kungiyoyin 'yan ta'addan na kara baje kolinsu ba, har ma suna amfani da dabaru da sabbin makamai na soja wajen yakar dakarun tsaro.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China