Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Babban magatakardan MDD ya nuna imani kan kasar Sin game da cimma nasarar yaki da cutar numfashi ta COVID-19
2020-02-17 12:28:59        cri

A jiya Lahadi ne, babban magatakardan MDD Antonio Guterres, ya bayyana a birnin Islambad, fadar mulkin kasar Pakistan cewa, kasar Sin ta cimma nasarori da dama wajen yaki da cutar numfashi ta COVID-19, kana yana da imani kan kasar Sin, wajen cimma nasarar yakin baki daya.

A wannan rana, Mr. Guterres ya kai ziyara a kasar Pakistan, inda ya kuma halarci taron manema labarai cikin hading gwiwa da ministan harkokin wajen kasar Shah Mahmood Qureshi. A yayin taron, Mr. Guterres ya ce, matsalar yaduwar cutar numfashi ta COVID-19 ta haifarwa kasar Sin babban kalubale, kuma matakan da kasar Sin ta dauka na yaki da cutar, sun nuna babban karfinta, wadanda suka kuma burge kasashen duniya sosai.

Mr. Guterres ya ce, "Akwai wuya matuka wajen fitar da dabara daidai cikin sauri karkashin irin wannan matsala mai tsanani", ya kuma kara da cewa, gwamnatin kasar Sin, ta yi kokari matuka wajen yaki da cutar, kuma muna cike da imanin cewa, tabbas cutar za ta ragu bi da bi, bisa kokarin da gwamnatin kasar Sin take yi. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China