Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Babban jami'in MDD ya bayyana yakini dangane da yakin da kasar Sin ke yi da cutar Corona
2020-02-15 16:55:40        cri
Jorge Chediek, daraktan ofishin MDD a kungiyar kawancen kasashe masu tasowa, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, nan bada dadewa ba, kasar Sin za ta shawo kan matsalar da take fuskanta na barkewar cutar Corona.

Jorge Chadiek, wanda kuma shi ne wakilin Sakatare Janar na MDD a kungiyar, ya ce yana da yakinin kasar Sin za ta shawo kan wannan annoba nan bada dadewa ba, sannan ta kara karfi fiye da baya.

Ya ce suna alfahari da da yadda kasar Sin ke tunkarar annobar, da kuma yadda take zama abun koyi ga sauran sassan duniya, wanda kuma alamu ne na karfin shugabanci da kasar Sin ke nunawa a fannoni daban daban na ci gaba. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China