Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaban Iran ya yaba wa Sin kan yakin da take yi da cutar numfashi ta COVID-19
2020-02-17 10:22:40        cri
Yayin taron manema labaran da aka yi a jiya Lahadi, shugaban kasar Iran Hassan Rouhani ya bayyana cewa, kasar Sin ta dauki nauyinta na hana yaduwar cutar numfashi ta COVID-19 yadda ya kamata, ta kuma yi bayani ga al'ummomin Sin da na kasashen duniya game da wannan cuta a kan lokaci, kuma lallai kasar Sin ta yi iyakacin kokarinta wajen yaki da cutar.

A sa'i daya kuma, ya ce, kasar Sin da kasar Iran suna da dangantaka mai kyau, ko da a lokacin da kasar Iran take fama da takumkumi mai tsanani da aka kakkaba mata, kasar Sin ta ci gaba da kiyaye dangantakar dake tsakaninta da kasar Iran yadda ya kamata, musamman ma kan batutuwan dake shafar yarjejeniyar nukiyar kasar Iran. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China