2020-02-10 09:56:20 cri |
Babban darektan hukumar lafiya ta duniya (WHO) Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya bayyana cewa, duniya ta yaba matuka da kwazon ma'aikatan lafiya a kasar Sin, musamman a lardin Hubei, wajen gano yadda za a kula da marasa lafiyan da suka kamu da annobar Corona da ma hana yaduwar cutar.
Tedros wanda ya bayyana haka a jiya Lahadi, ya kuma jinjinawa dubban ma'aikatan lafiya dake kasar Sin, musamman a lardin Hubei wadanda ke kula da marasa lafiya da tattara muhimman bayanai game da kwayar cutar Corona da ta bulla a kasar domin nazarin kimiyya, duk da matsin lambar da suke fuskanta.
Ya ce, duniya ta yaba kokarin ku, wajen gano yadda za a kula da marasa lafiyan da suka kamu da wannan annoba yadda ya kamata, da ma hana yaduwar kwayar cutar. Ya kuma bayyana cewa, masana a fannin magani da kimiyya suna aiki ba dare ba rana don ganin bayan wannan cuta.(Ibrahim)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China