Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaban Zimbabwe ya yabawa Sin game da matakan yaki da cutar coronavirus
2020-02-16 15:41:24        cri

A jiya, shugaban kasar Zimbabwe Emmerson Mnangagwa ya yabawa kasar Sin bisa kokarinta na daukar matakan yin kandagarki da kuma yaki da cutar numfashi ta coronavirus, kana ya yi imani cewa, kasar Sin za ta cimma nasarar shawo kan cutar.

Bayan da ya saurari yanayin yaki da cutar da matakan magance cutar a kasar Sin da jakadan Sin dake kasar Zimbabwe Guo Shaochun ya gabatar, shugaba Mnangagwa ya bayyana cewa, bayan barkewar cutar coronavirus, jama'ar kasar Sin sun yi kokari tare wajen tinkarar cutar, da samun babban ci gaba kan hana yaduwar cutar. Ban da wannan kuma, Sin da Zimbabwe suna kara yin hadin gwiwa don tabbatar da tsaro da moriyar jama'ar kasashen biyu. Ya zuwa yanzu, babu wani mutum da aka gano ya kamu da cutar a kasar Zimbabwe, wannan ne kyakkyawan sakamakon da kasashen biyu suka samu.

Shugaba Mnangagwa ya kara da cewa, ya yi imani Sin za ta cimma nasarar yaki da cutar, kasarsa ta Zimbabwe za ta samar da goyon baya da gudummawa ga kasar Sin. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China