Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin na goyon bayan cire takunkuman da aka sanyawa Zimbabwe ba tare da bata lokaci ba
2020-01-13 09:17:34        cri

Mamban majalisar gudanarwar kasar Sin, kuma ministan harkokin wajen kasar, Wang Yi, ya ce kasarsa na ba da cikakken goyon baya ga kiran da Zimbabwe da sauran kasashen Afrika suka yi, na neman a cire takunkuman da aka sanyawa Zimbabwe, ba tare da bata lokaci ba.

Wang Yi ya bayyana haka ne, yayin wani taron manema labarai da ya gudana jiya a Harare, babban birnin kasar Zimbabwe, tare da ministan harkokin waje da kula da cininkayya na kasar, Sibusiso Moyo.

Ministan ya ce, yin gaban kai wajen kakabawa Zimbabwe takunkumai da wasu kasashe da hukumomi suka yi, ba shi da wata hujja bisa tsarin dokar kasa da kasa, kuma ya keta muradun da halaltattun 'yancin kasar na samun ci gaba. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China