2019-08-25 15:14:27 cri |
A karon farko tawagar lokitoci ta 17 da gwamnatin kasar Sin ta tura kasar Zimbabwe ta kebe wurin nuna magungunan sha na gargajiyar kasar a bikin baje kolin kayayyakin aikin gona na Zimbabwe na shekarar 2019, bisa gayyatar da ma'aikatar kiwon lafiyar Zimbabwe ta yi mata.
A ranar 23 ga wata, uwargidan shugaban kasar Zimbabwe kuma jakadiyar kiwon lafiya da kula da yara ta kasar Auxilia Mnangagwa ta je wurin domin kallon magungunan sha na gargajiyar kasar Sin, inda likitocin kasar Sin suka yi mata bayani kan yanayin da magungunan sha na gargajiyar kasar Sin ke ciki yanzu, kana sun nuna mata fasahar jinya ta hanyar sa allura kan jikin mutane, madam Auxilia ta yi mamaki matuka kan fasahar, kuma ta bayyana cewa, tana fatan kasashen biyu wato Sin da Zimbabwe za su kara karfafa cudanya da hadin gwiwar dake tsakaninsu a bangaren likitancin gargajiya, ta yadda al'ummun kasarta za su amfana da sakamakon da likitancin gargajiyar kasar Sin ya kawo musu.
Yayin bikin baje kolin, wajen baje kolin magungunan sha na gargajiyar kasar Sin ya jawo hankalin al'ummun kasar Zimbabwe matuka, har ya kasance wata kafar yin bayani kan ilmomin magungunan sha na gargajiyar kasar Sin ga al'ummun kasar, ko shakka babu zai taimakawa ci gaban yaduwar magungunan a kasar ta Zimbabwe.(Jamila)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China