Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jamiin MDD ya bukaci a guji yada jita jita game da cutar coronavirus da kuma jaddada muhimmancin hada kai
2020-02-09 17:00:52        cri

Shugaban babban taron MDD karo na 74 Tijjani Muhammad-Bande a jiya Asabar ya bukaci a guji yada duk wata jita jita ko amfani da bayanan da ba na hukuma ba game da annobar cutar numfashi ta novel coronavirus, yayin da ya jaddada muhimmancin hada kai da juna daga dukkan fannoni a yanayin da ake ciki a halin yanzu.

Muhammad-Bande, wanda ya halarci taron kolin kungiyar tarayyar Afrika karo 33 a Addis Ababa dake gudana tsakanin 9 zuwa 10 ga watan Fabrairu, yace nuna goyon baya, da amfani da hanyoyin kimiyya, da bada tallafin kudade, su ne kadai hanyoyin da za su tsame al'umma daga halin da ake ciki a yanzu, inda ya buga misali da nasarar da aka samu wajen dakile annobar Ebola ta hanyar hada kai da juna.

Muhammad-Bande ya bukaci a gaggauta samar da muhimman bayanai ba tare da rufa rufa ba kuma akan lokaci, kana ya yabawa kokarin da mahukuntan kasar Sin suke aiwatarwa wajen dakile annobar. (Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China