Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Najeriya tana aiki tukuru wajen gano musabbabin bullar wata bakuwar cuta a kasar
2020-02-13 10:17:44        cri
Wani jami'i a Najeriya ya ce gwamnatin kasar tana aiki tukuru domin gano dalilin da ya haifar da bullar wata bakuwar cuta da ta barke wadda ta yi sanadiyyar kashe rayuka a jihar Benue dake shiyyar arewa ta tsakiyar Najeriyar.

Chikwe Ihekweazu, shugaban cibiyar yaki da yaduwar cutuka ta kasar (NCDC), da yake karin haske game da cutar wacce har yanzu ba'a tantance dalilan bullarta ba, ya ce tawagar jami'an dake aikin bayar da daukin gaggawa na kasar suna taimakawa gwamnatin jihar wajen binciken musabbabin bullar cutar wadda ta kashe mutane a yankin Obi na jihar Benue.

Cutar ta bulla a yankin ne makonni ukun da suka gabata kuma har ta yi sanadiyyar hallaka mutane hudu.

Dan majalisar dattijai mai wakiltar Benue ta kudu, Abba Moro, ya gabatar da batun a zauren majalisar inda ya bayyana cewa cutar ta hallaka mutane 15 sannan mutane 104 suna kwace a asibiti don a ba su kulawa.

Ihekweazu ya ce ana cigaba da duba yanayin wadanda suka kamu da cutar. Kuma an yi musu gwaje gwaje na cutar zazzabin Lassa da na zazzabin Yellow fever amma sakamakon bai nuna suna dauke da cutukan ba. A cewar Ihekweazu, suna jiran samun cikakken sakamakon karshe na gwaje gwajen. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China