2020-02-13 09:55:31 cri |
A cewar babban bankin kasar manyan dillalai a fannin hada hadar kudaden sun samu dala miliyan 100, yayin da kananan da matsakaitan kamfanoni sun samu kimanin dala miliyan 55 tun a ranar Talatar da ta gabata.
Sai kuma kwastomomi dake bukatar kudaden kasashen waje domin biyan kudaden makaranta, da kudaden magunguna, da sauran muhimman kudaden ziyara zuwa ketare sun samu dala miliyan 55, a cewar babban bankin na Najeriya.
Sanarwar bankin na CBN ta kara da cewa, mafunar daukar wannan mataki shi ne domin tabbatar da inganta fannin kasuwannin hada hadar kudaden kasar da kuma samun daidaituwar al'amurra wajen cigaban fannin musayar kudade a kasar.
Bugu da kari, babban bankin Najeriyar ya ce an dauki wannan mataki ne don samar da damammakin biyan muradun al'ummar kasar a fannin samun kudaden musaya na kasashen waje.(Ahmad Fagam)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China