2020-02-11 11:26:05 cri |
A cikin rahotonsa, jakada Zhou ya ce, yaki da annobar, aiki ne mafi muhimmanci da gwamnatin kasar Sin take himmantuwa a kai. Kasar Sin ta sauke nauyinta yadda ya kamata, ta kuma dauki matakai masu dacewa ba tare da bata lokaci ba kuma ba tare da rufa-rufa ba, lamarin da ya samu amincewa daga kasashen duniya.
Annoba tana da hadari, amma jita-jita da tsoro sun fi hadari. Wasu kasashen da suka hada da Nijeriya suna kara karfinsu na gurfanar da wadanda suke yada jita-jita a gaban kotu.
Ranar 10 ga watan Febrairun bana, rana ce ta cika shekaru 49 da kulla huldar jakadanci a tsakanin Sin da Nijeriya. A shekarun baya, huldar da ke tsakanin kasashen 2 ta bunkasa cikin sauri, wadda ta kawo wa jama'ar kasashen 2 alheri sosai. A 'yan kwanakin baya, gwamnati da al'ummar Nijeirya suna mara wa kasar Sin baya ta hanyoyi daban daban wajen yaki da annobar. Gwamnatin Sin da jama'ar kasar na gode musu sosai.
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China