Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
AU ta bukaci amfani da yarjejeniyar AfCFTA wajen cimma burin hana karar bindiga a Afirka
2020-02-07 12:25:11        cri
Kwamishinan kungiyar tarayyar Afirka ta AU mai lura da harkokin cinikayya da masana'antu Muchanga Albert, ya ce amfani da yarjejeniyar kafa yankin cinikayya maras shinge ta Afirka ko AfCFTA a takaice, zai taimaka wajen cimma nasarar hana jin karar bindigogi a sassan nahiyar Afirka, matakin da zai haifar da samuwar arziki da wadata ga dukkanin nahiyar.

Taken babban taron kungiyar AU karo na 33 dake gudana a helkwatar kungiyar dake birnin Addis Ababa na kasar Habasha shi ne, "Hana jin karar bindiga: samar da managarcin yanayin ci gaban Afirka."

Yayin wata zantawa da manema labarai a jiya Alhamis, Mr. Muchanga Albert, ya ce "Masu rajin kare manufar cinikayya cikin 'yanci sun dade suna nuna alfanunta, ta sauran fannoni ba wai kawai fannin raya tattalin arziki ba, masu mahanga na ganin cewa, cinikayya maras shinge na karfafa gwiwar al'umma da kasashe, wajen gudanar da cudanya cikin yanayi na zaman lafiya, suna kuma ganin manufar, a matsayin daya daga hanyoyin 'yantar da kasashe, ta hanyar baiwa wasu damar samar da hajoji da hidimomi, yayin da wasu kuma ke iya samun damar cin gajiyar hakan". (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China