Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin ta ba da rahoton sabbin mutane 2,478 da suka kamu da cutar Corona, 108 kuma sun mutu
2020-02-11 10:03:44        cri
Hukumomi lafiya na kasar Sin, sun bayyana a yau Talata cewa, sun samu rahoton sabbin mutane 2,478 da aka tabbatar sun kamu da cutar nunfashi, kana wasu 108 daga larduna 31 na kasar gami da rundunar sojoji ma'aikatan sa-kai a yankin Xinjiang sun mutu a jiya Litinin sanadiyyar cutar.

Ya zuwa jiya Litinin kuma, akwai kuma wasu karin mutanen 3,536 da ake kokarin tantance matsayin su na kamuwa da wannan cuta.

A cewar hukumar lafiyar kasar, ya zuwa jiya litinin, baki dayan yawan mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar a babban yankin kasar Sin, sun kai 42,638 kana mutane 1,016 sun mutu sanadiyyar cutar.

Bisa jimilla, an sallami mutane 3,996 daga asibiti bayan sun warke daga cutar. Sa'an nan ya zuwa jiya Litinin, an tabbatar da kamuwar mutane 42 ciki har da mutum guda da cutar ta halaka a yankin musamman na Hong Kong. Akwai kuma mutane 10 da aka tabbatar sun kamu da cutar a yankin Macao sai mutane 18 a yankin Taiwan.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China