Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kwararru daga WHO za su iso kasar Sin domin shiga aikin dakile cutar coronavirus, in ji NHC
2020-02-10 19:49:19        cri
Kakakin hukumar lafiya ta kasar Sin Mi Feng, ya ce wasu kwararru daga hukumar lafiya ta duniya WHO, za su iso kasar Sin domin shiga aikin dakile yaduwar cutar coronavirus da ake fama da ita.

Jami'in ya bayyana hakan ne a Litinin din nan, yayin wani taron manema labarai da ya gudana, yana mai cewa Sin da hukumar WHO, za su hada wata tawagar aiki ta kwararru, wadanda za su zurfafa tattaunawa, da fayyace yanayin da ake ciki game da bullar wannan annoba, da ma hanyoyin dakile ta.

Ana sa ran za su bayar da shawarwari game da hanyoyin kandagarki, da na shawo kan cutar ta coronavirus a Sin, da ma sauran kasashen da cutar ta bulla a mataki na gaba. Nan gaba a yau din ne kuma, ake sa ran tawagar farko ta jami'an hukumar WHO za su iso birnin Beijing, domin tattaunawa game da tsarin hadin gwiwa da za a yi da tsagin kasar ta Sin. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China