2020-02-10 20:15:13 cri |
Mi Feng ya bayyana hakan ne, yayin wani taron manema labarai na hadin gwiwa, karkashin shirin hadaka na majalissar gudanarwar kasar, wanda aka dorawa alhakin lura da aikin tabbatar da kandagarki, da kuma shawo kan cutar.
Mi Feng, ya ce a baya bayan nan, alkaluman warkewar masu fama da cutar a fadin kasar, sun kai kaso 8.2 bisa dari, sama da kaso 1.3 bisa dari da aka samu a ranar 27 ga watan Janairun da ya gabata. A lardin Hubei kadai, alkaluman wadanda suka warke a wannan gaba ya kai kaso 6.1 bisa dari, wanda ya haura kaso 1.7 bisa dari da aka samu a ran 27 ga watan Janairu.
Ya ce a birnin Wuhan kadai, adadin ya kai kaso 6.2 bisa dari, sama da kaso 2.6 bisa dari da aka samu a ranar 27 ga watan Janairu. Bugu da kari, fadada sassan ayyukan jinya ta hanyar samar da karin jami'ai, da samar da karin gadajen kwantar da marasa lafiya a lardin Hubei da birnin Wuhan, sun taimaka matuka wajen samar da karin nasarori. (Saminu)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China