Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Li Keqiang: ya kamata a yaki cutar numfashi ta hanyar kimiyya da fasaha
2020-02-10 10:09:26        cri

A jiya ne, firaministan kasar Sin Li Keqiang ya yi tattaki zuwa cibiyar nazarin cututtuka ta kwalejin ilmin likitanci ta kasar Sin, inda ya yi bincike kan yanayin nazarin cutar numfashi, tare da gaida masu nazari a cibiyar.

A jawabinsa shugaban kwalejin, ya yi bayani game da ci gaban da aka samu wajen magance da ma yaki da cutar numfashin da ta bulla a kasar, Li Keqiang ya yi na'am da kokarin da masu nazarin suke yi da ci gaban da suka samu, ya bayyana cewa, akwai bukatar dukkan jama'ar kasar Sin su hada kai don yaki da cutar, kana akwai bukatar amfani da matakai na kimiyya da fasaha wajen yaki da cutar. Ya ce ya kamata a yi nazari da kara yin hadin gwiwa don yaki da cutar ta hanyar kimiyya da fasaha.

Li ya kara da cewa, ya kamata masu nazari su gabatar da sakamakon nazarinsu game da hanyoyin yaduwar cutar da sauransu da jama'ar kasar suke sa lura don magance yaki da cutar yadda ya kamata. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China