Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Adadin wadanda suka kamu da cutar numfashi ya kai mutum 1,287
2020-01-25 15:59:09        cri
Hukumomin lafiya a kasar Sin sun tabbatar da rasuwar mutane 41, yayin da aka hakkake da cewa mutane 1,287 sun harbu da cutar numfashin nan, wadda kwayoyin cuta na coronavirus ke haddasawa.

An fitar da wadannan alkaluma ne dai da almurun ranar Juma'a, inda aka ce cikin jimillar wadannan marasa lafiya, 237 na cikin matsanancin yanayi.

Hukumar lafiyar ta ce jimillar masu dauke da cutar ya kunshi mutane 39 daga lardin Hubei na tsakiyar kasar, da mutum guda a Hebei, da kuma wani mutumin na daban a lardin Heilongjiang dake arewa maso gabashin kasar. Kawo yanzu kuma an gabatar da rahoton mutane 1,965 da ba a kai ga tantance ko sun harbu da cutar ba tukuna. A daya hannun kuma, akwai mutane 38 da suka warke bayan kamuwa da cutar, tuni kuma aka sallame su daga asibiti.

A wajen kasar Sin kuwa, an samu bullar cutar a kasashen Thailand, inda mutane 4 suka kamu, 2 kuma suka warke. Sai Japan inda mutane 2 suka harbu kuma mutum guda ya warke 1. Akwai kuma Koriya ta kudu, da Amurka, da Vietnam da Faransa masu mutane biyu-biyu. Sai kuma Singapore mai mutane 3, da Nepal mai mutum 1. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China