Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
WHO: Har yanzu cutar nunfashi da ta bullo a kasar Sin ba ta zama barazana ga harkar kiwon lafiyar kasa da kasa ba
2020-01-24 14:21:16        cri
Hukumar lafiya ta duniya (WHO) ta bayyana a jiya Alhamis cewa, har yanzu da sauran lokaci, kafin a ayyana cutar nunfashi wadda kwayar "coronavirus" ke haddasa da ta bulla a kasar Sin a matsayin barazana ga harkar kiwon lafiyar kasa da kasa.

Sai dai hukumar ta yi gargadin cewa, yawan wadanda suka kamu da cutar na iya karuwa, duba da yadda aka kasa fahimtar kwayar cutar.

Babban darektan hukumar Tedros Adhenon, ya ce, ya kamata a mayar da hankali, koda yake wannan batun gaggawa ne a kasar Sin. Amma dai har yanzu cutar ba za ta zama barazanar lafiya ga kasa da kasa ba. Ya ce tawagar hukumar take sa-ido ta bayyana cewa, cutar da ta bulla a kasar Sin tana da hadari matuka, a kasar da shiya da ma duniya baki daya.

WHO dai ta yanke shawarar rashin ayyana cutar a matsayin barazana ga harkar kiwon lafiyar kasa da kasa, a matsayin abin da ba a saba ba, bisa la'akari da yadda hakan ka iya haifar da matsalar lafiya ga sauran kasashe ta hanyar watsa cutar a duniya da ma neman taimakon kasa da kasa don magance ta.

Tedros ya bayyana cewa, yanzu haka an sanar da hukumar game da rahoton mutane 584 da suka kamu da cutar, ciki har da mutane 17 da suka mutu. Baki daya mutane 575 ne suka kamu da cutar, kuma dukkan wadanda suka mutu a kasar Sin ne, an kuma an ba da rahoton bullar cutar a kasashen Japan, da Koriya ta kudu, da Singapore da Thailand da Amurka da kuma Vietnam.

Ya ce, ya yi imani kasar Sin ta dauki matakan da suka dace na hana yaduwar kwayar cutar coronavirus a Wuhan, inda cutar ta bulla, da sauran biranen kasar. WHO tana fatan cewa, matakan da kasar Sin ta dauka na ganin bayan wannan cuta, za su yi tasiri matuka.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China