Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta fitar da rahoton kamuwar mutane 571 da cutar numfashi
2020-01-23 15:56:45        cri
Hukumomin lafiya na kasar Sin, sun fitar da rahoton kamuwar mutane 571 da cutar numfashi, wadda kwayoyin cutar "coronavirus" ke haddasawa. An kuma ce ya zuwa daren ranar Laraba, cutar ta yadu zuwa yankunan larduna 25 na kasar.

Rahotanni sun bayyana cewa, tuni aka gabatarwa hukumar kiwon lafiya ta kasar NHC da rahoton kamuwar mutane 393 da wannan cuta mai hadari. Ya zuwa yanzu dai mutane 17 ne aka tabbatar da rasuwar su, bayan sun karbu da cutar, kuma dukkanin su a lardin Hubei. An ce wadanda suka rasun na tsakanin shekaru 48 da 89 ne.

A cewar hukumar NHC, mafi yawan wadanda suka rasun da ma suna fama da wasu cututtukan na daban, kamar cutar hanta, ko cutar sikari, ko hawan jini ko matsananciyar cutar zuciya.

A yankunan dake wajen babban yankin kasar Sin kuwa, an samu rahoton bullar cutar a yankunan Hong Kong, da Macao, da Taiwan na kasar Sin, da kuma kasar Amurka. Sauran sun hada da kasashen Japan, da Koriya ta Kudu inda aka samu mai kamuwa da cutar daidaya, yayin da a Thailand cutar ta kama mutane 3.

Bisa jimilla, an yi hasashen mutane 5,897 sun yi cudanya ta kusa da wadanda suka kamu da cutar, kuma hukumar NHC ta ce cikin wannan adadi, ana kan lura da lafiyar jikin mutane 4,928, yayin da aka sallami mutane 969, wadanda aka tabbatar da cewa ba su kamu da cutar ba.

Har ila yau, NHC na fitar da bayanai game da matakan kandagarki, da na dakile yaduwar cutar yadda ya kamata. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China