2020-01-22 10:50:59 cri |
Mataimakin ministan kasuwanci na kasar Sin Qian Keming ne ya bayyana haka a jiya Talata, inda ya kara da cewa, a shekarar 2019, kasar Sin ta samu damar yin amfani da jarin da wasu kamfanonin kasashen waje suka zuba mata, wanda yawansa ya kai Yuan biliyan 941.5 (kwatankwacin dalar Amurka biliyan 136.4), wanda ya karu da kashi 5.8% bisa na bara, kuma ya kai matsayin koli a tarihi.
Wannan adadi ya sa kasar Sin ta ci gaba da zama kasa mafi janyo jarin waje ta biyu a duniya. A cewar jami'in, ana ta kokarin inganta tsarin amfani da jarin waje a kasar Sin, yayin da wasu kasashen dake da tattalin arziki mai ci gaba, suke kokarin zuba karin kudade ga kasuwannin kasar. (Bello Wang)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China