Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Babban jami'in kasar Sin ya gana da wasu shugabannin MDD masu kulawa da ayyukan kwaskwarimar kwamitin sulhu
2020-01-22 10:44:51        cri
Mamban ofishin siyasa na kwamitin tsakiya na jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin, kana darektan ofishin kwamitin tsakiya mai kula da harkokin waje Yang Jiechi, ya gana da shugabannin babban taron MDD karo na 74, masu kula da kwaskwarimar kwamitin sulhu, musamman ma a fannin tsarin gudanar da shawarwari tsakanin gwamnatoci, a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin, a jiya Talata. Manyan jami'an MDDr biyu su ne, wakilin dindindin na UAE a MDD Lana Zaki Nusseibeh, da Wakiliyar kasar Poland a Majalisar Joanna Wronecka.

Yang Jiechi ya ce, makasudin yin kwaskwarima kan kwamitin sulhun shi ne, karfafa iko, da kuma ingancin tsarin aiki na kwamitin, da kara wakilcin kasashe masu tasowa, da kanana da matsakaitan kasashe don fito da muryarsu, da kuma nuna yanayin dimokiradiyya na dangantakar kasa da kasa, da na cudanyar bangarori daban daban a duniya.

Ya ce kasar Sin za ta nuna goyon baya sosai ga aikin shugabannin biyu, tare da tabbatar da cewa, garambawul din ya kasance a kan wata hanyar da ta dace da kundin MDD, da kuma moriyar bai daya ta kasashe mambobin majalisar.

A nasu bangare, Lana Nusseibeh da Joanna Wronecka sun bayyana cewa, sun dora muhimmanci kan matsayin kasar Sin, da kuma rawar da take takawa wajen sake fasalin kwamitin sulhun. Jami'an sun ce yin shawarwari tsakanin gwamnatoci, babbar hanya ce da kasashe mambobin MDD suke bi don neman tabbatar da harkoki masu alaka da kwaskwarima ga tsarin kwamitin sulhu, don haka jami'an biyu, suna kokarin kare wani yanayi na tattaunawa, da musayar ra'ayi tsakanin dukkan bangarori na masu ruwa da tsaki. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China