Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasashe 5 sun samu wakilcin wucin gadi na kwamatin MDD
2020-01-03 09:20:39        cri
Daga jiya Alhamis kasashen Estonia, Nijer, Saint Vincent da Grenadines, Tunisia da Vietnam sun zama wakilan wucin gadi a kwamitin sulhun MDD.

Kasashen biyar za su shafe wa'adin shekaru biyu. Daga cikin sabbin kasashen biyar da aka zaba a matsayin mambobin kwamitin, Estonia, da Saint Vincent da Grenadines, ba su taba yin wakilcin kwamitin sulhun MDDr ba.

Kasashen Kuwait, Peru, Poland, Kwadibuya, da Equatorial Guinea sun fice daga kwamitin sulhun.

Kwamitin sulhun MDD mai mambobin kasashe 15 yana kunshe da wakilan mambobin kasashen dindindin biyar, da suka hada Birtaniya, Sin, Faransa, Rasha da Amurka, da kuma wasu wakilan kasashe 10 na wucin gadi wadanda ake zabarsu a lokacin babban taron MDD don yin wakilci na wa'adin shekaru biyu. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China