Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sakatare Janar na MDD ya bayyana cewa akwai kyakkyawar fata tattare da matasa
2019-12-31 10:14:28        cri
Sakatare Janar na MDD Antonio Guterres, ya ce yayin da ake shiga sabuwar shekara a lokacin da ake fuskantar rashin tabbas da rashin tsaro a fadin duniya, akwai kyakkyawan fatan samar da sauyi daga matasa.

A wani sakon bidiyo domin sabuwar shekara, Sakatare Janar din ya ce sauyin yanayi ba matsala ce dake da nisan zango ba kadai, domin matsala ce dake bayyane kuma ake fuskanta a yanzu, yana mai cewa ba zai yiwu su zama wadanda suka yi sake duniya ta kone ba.

Sai dai ya ce akwai kyakyawar fata, yana mai cewa sakonsa na sabuwar shekara na zuwa ne ga matasan fadin duniya, a matsayinsu na wadanda ake kyautatawa zato. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China