Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jami'in MDD ya koka game da jinkiri da Amurka keyi na bada visa ga wakilan kasashen duniya
2019-12-27 15:16:31        cri
Babban sakataren MDD Antonio Guterres ya bayyana matukar damuwa bisa ga jinkirin da Amurka ke yi wajen bayar da takardun visa ga wakilan kasashen Rasha, da sauran kasashe mambobin MDD dake halartar taron MDDr a birnin New York.

Watanni da dama da suka gabata, Guterres da masana harkokin shari'a na MDD sun sha gabatar da damuwarsu, har ma da matsayar da MDD ta dauka, ga manyan jami'an kasar Amurka, inji kakakin MDD Stephane Dujarric a wata sanarwar da aka rabawa manema labarai.

Ya ce babban sakataren MDDr tare da sauran tawagarsa za su ci gaba da bibiyar al'amarin.

A wani taron kwamitin MDD game da kasashen da abin ya shafa, kasashen Rasha, Cuba da Syria suna daga cikin mambobin kasashen da suka daga murya game da batun jan kafa wajen ba su visar zuwa kasar ta Amurka. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China