Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin da Ghana sun sanya hannu kan yarjejeniyar hadin-gwiwa a fannonin tattalin arziki da fasaha
2019-12-13 09:51:34        cri
Jakadan kasar Sin a Ghana Wang Shiting, da ministan kudin kasar Ghana Kenneth Ofori-Atta, sun sanya hannu kan wata yarjejeniyar hadin-gwiwa a fannonin da suka shafi tattalin arziki da fasaha.

A cewar Wang Shiting, karkashin yarjejeniyar da aka rattabawa hannu a jiya Alhamis, Sin za ta samar da rancen kudi da yawansu ya kai yuan miliyan 300, kwatankwacin dalar Amurka miliyan 42.6, wadanda Ghana za ta yi amfani da su, wajen zartas da ayyukan dake kunshe cikin yarjejeniyar da sassan biyu suka kulla.

Jakadan ya ce akwai labarai masu dadin ji, game da ayyukan hadin gwiwa dake wakana tsakanin Sin da Ghana. Ya ce a 'yan watannin baya bayan nan ma, sassan biyu sun kaddamar da aikin madatsun ruwa, wanda kamfanonin Sin za su aiwatar, baya ga kaddamar da aikin gina kwalejojin fasaha, da na koyar da sana'o'i, da cibiyoyin horaswa da aka daga darajarsu a kasar ta Ghana.

Wang Shiting ya kara da cewa, Sin za ta yi amfani da ikonta, da basirarta, wajen tallafawa Ghana, ta yadda za ta kai ga matsayin "kasar da ke iya wadatuwa da kanta". (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China