Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jami'in WTO yana fatan taron kolin G20 zai magance takaddamar ciniki
2019-06-21 10:56:08        cri

Babban daraktan kungiyar ciniki ta duniya (WTO) Roberto Azevedo ya fada a jiya Alhamis cewa wakilan kungiyar WTO suna fatan taron kolin da za'a gudanar na kasashen G20 a Japan a makon gobe zai warware matsalar takaddamar ciniki.

"Muna kallon yadda takaddamar ciniki take kara zafafa kuma an zura ido ana kallo, kuma wannan koma baya ne ga bunkasuwar kasuwancin duniya," jami'in na WTO ya yi wannan gargadi ne a taron manema labarai wanda kungiyar 'yan jaridu ta MDD (ACANU) ta shirya a Geneva.

Azevedo ya kara da cewa, "Kowa da kowa yana fatan za'a magance takaddamar cinikayya ta duniya".

Za'a gudanar da taron na kasashen G20 ne a ranakun 28-29 ga watan Yuni a Osaka na kasar Japan, kana Azevedo ya ce, a lokacin taron kolin G20 na baya wanda aka gudanar a Buenos Aires na kasar Argentina a watan Disambar shekarar 2018 shugabanni sun bukaci a yi sauye sauye a kungiyar ta WTO.

Jami'in ya ce, "Sun yi amanna cewa tsarin cinikayya yana da muhimmanci" kuma "suna son a sassauta matsalar takaddamar ciniki, domin a inganata da kuma kyautata tsarin cinikayyar".(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China