Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
MDD ta kadu da harin da aka kai cibiyar horar da wasan dawaki a babban birnin Libya
2019-10-07 15:42:34        cri

Shirin wanzar da zaman lafiya na MDD dake aiki a Libyan UNSMIL, ya ce ya kadu da harin saman da rundunar sojin gabashin kasar ta kai kan cibiyar horar da wasan dawaki dake Tripoli, babban birnin kasar.

Wata sanarwa da shirin UNSMIL ya fitar, ta ce ta fusata da luguden wuta ta sama da dakarun Janar Haftar suka kai cibiyar wasan dawaki dake unguwar Janzour na birnin Tripoli. Rahotanni sun ce, luguden wutan, wanda ya auku yau da rana, ya yi sanadin raunata wasu yara tare da lalata kayayyaki a wurin.

Shirin ya ce, ya tura tawagar masu nazari domin gano wurin da kuma yanayin harin.

Sanarwar ta ce, tawagar ta tabbatar da cewa jiragen yakin sun kai harin bama-bamai 4 kan cibiyar, wanda na farar hula ne, kuma babu wata kadara ko kayayyakin soji da ta gani a wurin.

Shirin ya kuma yi tir da harin tare da jadadda cewa, hare-hare kan fararen hula da kayayyakinsu ya keta dokokin jin kai na kasa da kasa da na hakkin dan Adam, kuma yana iya zama laifin yaki. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China