Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaban AL da manzon MDD sun bukaci a daidaita batun Libya ta hanyar siyasa
2019-09-03 10:30:28        cri

Babban sakataren kungiyar tarayyar kasashen Larabawa (AL) Ahmed Abul Gheit da manzon MDD na musamman kan Libya Ghassan Salame, sun tattauna kan yanayin siyasa da tsaro na baya-bayan nan da ake ciki a Libya, da matakan da suka dace na kawo karshen fadan da ake ci gaba da gwabzawa a kewayen Tripoli, babban birnin kasar.

Wata sanarwa da kungiyar AL ta fitar bayan ganawar, ta jaddada muhimmancin daukar matakan kawo karshen fadan da ake fafatawa, ta yadda za a kai ga tsagaita bude wuta kwata-kwata.

Jami'an biyu sun kuma jaddada cewa, mataki na siyasa ne kadai zai kawo karshen matsalar kasar da yaki ya wargaza, maimakon daukar matakin soja.

Abul Gheit ya nanata matsayin kungiyarsa na yin adawa da duk wani salo na tsoma hannun kasashen ketare cikin harkokin Libya.

Salame, ya kai ziyara Libya ne, don neman goyon bayan kasashen shiyyar da na kasa da kasa kan yadda za a magance matsalar kasar ta hanyar mataki na siyasa. Ya kuma bayyana cewa, ya kamata kungiyar AL ta shiga matakin warware matsalar kasar ta Libya ta hanyar siyasa.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China