Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An kwashe bakin haure 165 zuwa Najeriya daga Libya
2019-10-05 15:19:43        cri

Hukumar kula da bakin haure ta kasa da kasa (IOM) ta sanar cewa, kimanin bakin haure 165 ne suka mika wuya bisa radin kansu don kwashe su zuwa Najeriya daga kasar Libya.

Cikin wata sanarwar da hukumar IOM ta fitar ta ce, a jiya Juma'a jami'anta sun taimakawa bakin hauren kimanin 165 daga Najeriya dake gararamba a Libya, mafi yawansu mata ne da kananan yara, inda aka mayar da su gidajensu a wani jirgin sama da aka dauki hayarsa daga filin jirgin saman Sebha dake kudancin Libya.

Shirin mayar da bakin hauren kasashensu na ainihi, hukumar IOM ce ta tsara kwashe bakin hauren da suka shigo ta barauniyar hanya, inda suke gararamba a kasar Libya.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China