2019-10-07 15:00:57 cri |
Hukumomin gwamnatin Najeriya sun tabbatar da cewa, 'yan bindiga sun yi garkuwa da mutane 6 a wani kauye dake shiyyar arewa maso gabashin Najeriya, wanda ke kan iyakar Najeriya da Kamaru.
Wadanda lamarin ya rutsa da su fasinjoji ne dake wucewa ta babbar hanyar kauyen Gurin dake jihar Adamawa a shiyyar arewa maso gabashin Najeriya, a cewar wani dan majalisar dokokin yankin, Shuaibu Babas.
Babas, dan majalisar dokokin jihar Adamawa mai wakiltar yankin, ya shedawa 'yan jaridu faruwar lamarin, ya ce al'amarin ya tayar da hankalin al'ummar yankin.
Ya bukaci gwamnati da ta dauki matakan dakile yawaitar yin garkuwa da mutane, kana ya bukaci hukumomin tsaro da su kara kaimi wajen tsananta bincike don shawo kan matsalar.
A cewarsa, wadanda lamarin ya rutsa da su suna kan hanyarsu ne ta duba shanunsu a wuraren kiwo a yankin, inda masu garkuwar cikin manyan motoci suka yi awon gaba da su.
Kawo yanzu jami'an 'yan sanda ba su ce uffan ba game da faruwar lamarin.(Ahmad Fagam)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China