Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ambaliyar ruwa ta lalata gonaki sama da 3,000 a arewa maso yammacin Najeriya
2019-10-05 15:06:11        cri

Ambaliyar ruwa dake ci gaba da ta'azzara a shiyyar arewa maso yammacin Najeriya ta yi sanadiyyar lalata gonaki sama da 3,000, lamarin da ya haifar da mummunar hasara na kudaden shigar manoman yankunan, wata kungiyar manoman Najeriya ce ta sanar da hakan a jiya Juma'a.

A cewar shugaban kungiyar manoman Najeriya Yakubu Dolon-Zugo, a jahar Jigawa dake shiyyar arewa maso yammacin Najeriya sama da yankuna 11 ne ambaliyar ruwan ta shafa.

Dolon-Zugo ya ce, daga cikin kayayyakin amfanin gonar da suka salwanta sun hada da dawa, ridi, masara, auduga, shinkafa da dai sauransu.

Ya ce, kusan kashi 70 zuwa 80 na amfanin gonarsu ambaliyar ruwan ta lalata cikin watanni biyu, ya kara da cewa, manoman yankunan suna cikin tsananin bukatar agaji sakamakon hasarar da suka tafka na kudaden shigarsu.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China