Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Gwamnatin Sudan ta yi alkawarin goyon bayan masu sha'awar zuba jari a bangarorinta na mai da iskar gas
2019-10-01 09:29:14        cri

Gwamnatin Sudan ta yi alkawarin goyon bayan duk wanda ke sha'awar zuba jari a bangarorin mai da iskar gas na kasar.

Cikin wata sanarwa da ya fitar jiya, Minstan makamashi da hakar ma'adinai na kasar Adel Ali Ibrahim ya ce, suna maraba da duk wanda ke sha'awar zuba jari a bangaren haka da sarrafa man fetur, yana mai cewa lokacin kasuwanci da zuba jari a kasar ya kara kyautata fiye da baya.

Ministan ya kuma yi alkawarin karkashin sabuwa gwamnatin kasar, za a samar da kyakkyawan yanayi da kawar da duk wani tarnaki, domin jan hankalin masu zuba jari.

Sanarwa ta ce. Adel Ali Ibrahim ya bayyana haka ne a jiya Litinin, lokacin da yake ganawa da wakilan kamfanin mai na Dragon Oil na Hadaddiyar Daular Larabawa, tare da bitar sha'awar da kamfanin ya nuna ta zuba jari a bangarorin mai da iskar gas na kasar.

Sudan na neman kara yawan man da take samarwa na ganga 120,000 a kowacce rana, bayan ta rasa kaso 2 cikin 3 na man da take samarwa, biyo bayan ballewar Sudan ta Kudu a shekarar 2011. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China